Adadin wadanda suka mutu a wasu sabbin hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna ya karu daga 20 zuwa 38.
Kwamishinan tsaron da kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A ranar Lahadi da yamma ne Aruwan ya fitar da sanarwar manema labarai inda ya ce an kashe mutane 20, tare da kona dukiyoyi yayin harin.
Sai dai a wata sanarwa da aka sabunta ta ranar Lahadi da yamma, ta bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya karu daga 20 zuwa 38.
Ya bayar da sunayen al’ummomin da aka kai harin da suka hada da Kauran Fawa, Marke da Riheya.
Ya ce an gano 29 daga cikin wadanda harin ya rutsa da su yayin da sauran tara ba a tantance ba.
A cewarsa, wadanda ‘yan bindiga suka kashe sun hada da; Rabi`u Wada, Salisu Boka, Alh Nura Nuhu, Alh Bashari Sabiu, Alh Lawal Dahiru, Abbas Saidu, Inusa Kano, Malam Lawal Nagargari, Malam Aminu, Lawal Maigyad.
Sauran su ne; Alh Mustapha, Lawal Aliyu, Sale Makeri, Sani Lawal, Auwal Umar, Jamilu Hassan, Badamasi Mukhtar, Malam Jibril, Lawal Tsawa, da Sule Hamisu.
Sauran sun hada da Sadi Bala, Kabiru Gesha, Abubakar Sanusi, Saiph Alh Abdul, Haruna Musa, Lawal Hudu, Malam da Shuaibu Habibu da kuma Malam Yahaya Habibu da Abubakar Yusuf.
Ya kara da cewa, biyo bayan rahoton hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Idasu, karamar hukumar Giwa, kamar yadda yake kunshe a cikin wani bayani da ya gabata, hukumomin tsaro sun tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna cewa an kashe mutane 38 a duk wuraren da aka kai harin.
Ya ce, “An gano 29 daga cikin wadanda abin ya shafa, yayin da sauran tara ba a san ko su waye ba har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto.”