Reverend Godwin Okonkwo, mai aniyar tsayawa takarar gwamnan Jihar Anambra karkashin inuwar Jam’iyyar APC, ya ce muddin Jam’iyyar tasu na bukatar kaiwa gaci a zaben gwamna dake tafe nan gaba kadan, to lallai a shuka adalci a zaben fidda gwani.
To sai dai bisa ga dukkan alamu yana wanka ne mai kama da jurwayi, domin ya tabbatar da cewa muddin Jam’iyyar ta tsaida shi takarar, to ko shakku babu zai cire mata kitse a wuta.
Mista Okonkwo duk yana wadannan maganganu ne yayin da ya jagoranci wani taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a birnin Awka fadar gwamnatin jihar ta Anambra a yau Laraba.
Ya ce bisa irin yadda ya gudanar da tuntuba a dukkanin gundumomi 326 da ma ƙananan Hukumomi na Jihar, hakan ya bashi zummar ganin cewa shi kadai zai iya haurar da Jam’iyyar tasu izuwa tudun na-tsira.
Ya kara da cewa a matsayinsa na Waliyyin Allah, babu wani dan takara da ya kama kafarsa a tsoron Ubangiji, don haka shi ya kamata a ce jam’iyyar ta damka mishi wannan takara salun-alun.