zango

Adam a Zango ya yi ma Ali Nuhu da Dauda Rarara Kacha-Kacha Kan Batun Gasar Wakar Baba Buhari Dodar

Daga cikin manyan jaruman masanaantar shirya fina finan Hausa Adam A Zango ya yima Mawaki Dauda Kahutu Rarara da Jarumi Ali Nuhu Kacha-kacha kan batun bayar da kyaututtukan gasar wakar Baba Buhari Dodar. Jarumi Adam A Zango yace yasha suka daga wajen Jaruman da suka fafata a gasar da kuma wasu baadin mutane kan yadda aka yi son Rai wajen bayar da kyaututtukan gasar.

Adam A Zango, yace tabbas nine alkalin gudanarwa da kuma tantance Yan gasar kuma nayi na fitar da Mutane uku cikin wadanda suka fafata a matsayin zakarun da suka yi fice a gasar, sai dai lokacin bayar da kyaututtukan na tafi Bauchi aiki lokacin da aka gudanar da bikin bayar da kyautar a jihar Katsina.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar,Zango yace Saboda bana nan Dauda Rarara ya gayyaci su Ali Nuhu da su Lilisko suka yi yadda suke so kuma hakan bai dace ba, ina so inyi amfani da wannan dama in baiwa mutane hakuri cewar ni babu hannu na a cikin wadanda suka bayar da kyautan ga Wanda suke so kuma suka ga dama, ni bana gari su Ali Nuhu ne da Dauda suka yi abunda suke so. Ni na basu sunayen wadanda suka yi nasara a gasar kuma su kuma suka Ajiye su suka dauki wasu a lokacin bayar da kyaututtuka kuma banji dadin haka ba kuma ni ba haka nake tsari na ba; inji Zango. Mun mallaki Faifayin Bidiyon idan kuna bukata sai mu wallafa muku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *