Gwamnan Jahar Gombe Muhammad Yahaya a ranar Juma’a ya bayyana cewar addu’o’in mutanen Allah kamar su Shugaban Cocin Redeemed Christian Church Fasto Enoch Adeboye , da wasu, sun suke riƙa da Najeriya.
Yahaya wanda ya karɓi Shehin Kiristan a lokacin ziyarar Daya kawo masa, ya bukaci a cigaba da wadannan addu’o’i, inda ya yabawa Adeboye daya zabi matsayar zuwa jahar domin ziyara.
Adeboye yace jahar ne domin gangamin sa, daya shirya wa Kiristoci domin bikin murnar cikar sa shekaru 80.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’ar OAU Ta Gabatar Da Takardar Tuhuma Ga Mai Masaukin Baki Bayan Mutuwar Wata Daliba
Yahaya ya samu wakilci mataimakin sa Dr. Manassah Jatau, ya bayanna godiyar sa ga faston daya cika roƙon mabiyan sa, da kuma bin umarnin Allah tare da ziyartar Gombe.
Yace ” yawaitar matsaloli da Najeriya ke fuskanta na tsaro, da matsin tattalin arziki, dole wani aminta cewa addu’ar su Fasto Adeboye ce ke riƙe da Ƙasar.
Tunda Farko, Adeboye ya shaidawa wadanda suka tara taron cewa yazo Gombe ne domin girmama waɗanda suka shirya taro domin sa mai suna “Hasken Najeriya, domin bikin murnar cikar sa shekaru 80.