Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tsayar da Dr Akinwunmi Adesina a matsayin dan takarar shugaban Bankin ci gaban Afrika wato AfDB a takaice.
Akinwunmi, a yayin da yake jawabi a wani taro a Legas a ranar Lahadi, ya bayyana jindadinsa ga shugaba Buhari bisa zabarsa da ya yi a karo na biyu domin ganin an sake zabarsa a matsayin shugaban Bankin. A cewar Adesina, Nijeriya ta tallafa masa sosai.
Ya ci gaba da cewa; a lokacin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya zabe shi a matsayin Ministan Noma, ya ce; lamari ne da aka kira shi ya yiwa kasarsa ta haihuwa aiki. Ya ce; ya yiwa Nijeriya aiki a bisa iya karfinsa. Ya ce ya godewa Allah da ya zama bangaren sha’ani noma da kiwo na Nijeriya yana samun goyon baya da kwaskwarima yadda ya kamata.
Ya ce; sakamakon goyon bayan tsohon shugaban kasa Jonathan da shugaba Buhari ya sanya Nijeriya ta samu shugabancin Bankin ci gaban Afrikan. Ya ce; taimakon Nijeriya ya sanya shi zama shugaban Bankin.
Ya tabbatar da rawan da tsoffin shugabannin Nijeriya wanda ya hada da Janaral Abdulsalami Abubakar, Janaral Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar da Namadi Sambo, da kuma Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, a matsayin wadanda suka yi masa Kamfen. Inda ya ce cikin yardarm Allah ya zama shugaban Bankin a ranar 28 ga watan Mayun 2015, wato Awa ashirin da hudu bayan ya sauka a mukamin minista.
Ya ce Nijeriya ta yi matukar murna kasancewarsa shugaban Bankin na farko daga Nijeriya tun shekarar 1964.