Kungiyar Kwallon Kafan Super Eagles ta Najeriya ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Masar da ci 1-0 a wasan farko na rukunin D a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Garroua na kasar Kamaru.
Eagles ce ta zura kwallo daya tilo ta hannun dan wasan gaba na Leicester City, Kelechi Iheanacho wanda ya zura kwallo a ragar ta a minti na 30 da fara wasan.
Wasan farko ya ƙare 1-0 ga Eagles kuma a cikin wasan.
Wasan dai ya kare ne inda Masarawa da babban dan wasansu Mohammed Salah suka kasa yi wa Eagles barazana da mai tsaron gida, Maduka Okoye, ba tare da wani tabuka komai ba.