Bankin Raya kasashen Afirka (AfDB) ya ce zai kashe dala miliyan dari da goma ($110m) don samar da hanyoyi a karkara, wadan da su ne ababen more rayuwa na sufuri, da samar da ruwa da tsaftar muhalli da harkokin noma.
Shugaban Bankin Raya Afirka Dr Akinwumi Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa rasuwar Sani Dangote a gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Asabar.
Ya ce “Za Mu yi amfani da da dala miliyan 110 a Kano don shirinmu na yankin sarrafa masana’antu na musamman, muna da kusan dala miliyan 563 da za a sadaukar don yin wannan aiki a jihohi daban-daban na Najeriya.
Da wannan kudin da za a yi amfani da shi a jihar Kano ku yi tunanin abun da za mu iya yi. Zuba hannun jari a hanyoyin karkara, saka hannun jari kan ababen more rayuwa na sufuri, saka hannun jari a fannin ruwa da tsafta da kuma saka hannun jari a fannin noma don bunkasa samar da abinci.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar ya aikewar Dimokuradiyya, ta ce Bayan ya yaba da sauyin da gwamnatin Ganduje ta yi, Dr Adesina ya ce ya ji dadin tattaunawa da gwamnan kan ayyukan bankin raya Afirka a jihar.
Dakta Adesina ya kara bayyana cewa, “Tare da wannan shiri na daruruwan Dalar Amurka, zai taimaka wajen samar da ingantattun ababen more rayuwa a yankunan karkara.
Hakan zai baiwa kamfanoni masu zaman kansu damar rage yawan asarar da suke samu, da samar da sarkakiyar, da sauya yankunan karkara daga yankunan da ake fama da talauci zuwa yankin bunkasar tattalin arziki. Da kuma kara yawan albarkatun da jihar ke da su.”
A nasa jawabin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya godewa shugaban bankin raya kasashen Africa AfDB bisa wannan sabon cigaba da aka samu tare da bada tabbacin goyon bayansa da hadin kai domin samun nasarar aiwatar da aikin a dukkan matakai.
Ya ce “Wannan shi ne abin da muke nufi da cigaba na gaskiya, idan aka karfafa cibiyoyi kuma an yi wa daidaikun mutane ko tarin jama’a jagora.”
Gwamna Ganduje ya kuma godewa shugaban na AfDB kan yadda ya yaba da cigaban jihar. Cewa “Muna gode muku da bisa yabon kyakkyawan cigaban da muka samu tun lokacin da muka shiga ofishi a shekarar 2015.”
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Ganduje cewa “Na kasance Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na tsawon shekaru shida a lokacin mulkin Soja. Don haka ina tattaunawa da tsarin Master Plan na Kano. Kuma ina tattaunawa da abubuwan da ke cikin buranen Mega, da buranen Smart.
Don haka burina shine in tallata Kano zuwa Mega City. Kuma Mega City ba tarin yawan jama’a ba ne kawai. Tarin yanayi ne da abubuwan aiki, inda zirga-zirgar ababen hawa ke tafiya, inda ayyukan kiwon lafiya ke da kyau da nufin rage yawon shakatawa na likitanci a kasashen waje da kuma inda za ku iya samun tsaro ta amfani da fasahar zamani.”