Dan wasa Ahmed Musa zai dunga kwasar albashi dala miliyan 2.5 a duk shekara, wanda yayi dai dai da biliyan daya da dubu dari biyu, bayan ya kammala zama Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Fatih Karagumruk a kasar Turkiyya. Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Adai ranar Alhamis ne Dan wasa Ahmed Musa ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk har na tsawo shekaru biyu bisa Yarjejeniyar kara shekaru nan gaba.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk yace ” na yi sha’awar zuwan kungiyar ta Fatih Karagumruk ne saboda kudirin su, da kuma kyakykyawan manufarsu.”
KARANTA;-Shisha tafi Sigari cutarwa, Masana kiwon lafiya sunyi bayani
Ya cigaba da cewa ya shirya tsaf don ganin sauran abokanan wasan sa, su zo don su cigaba da baiwa Fatih Karagumruk gudummawa da iya karfin sa.
Wani babban abokin Dan wasan Ahmed Musa, yake shaidawa Jaridar Extra Sports, cewa kungiyar ta Fatih Karagumruk ta nemi Ahmed Musa ne saboda ganin ya buga wasanni daban-daban, irinsu gasar cin kofin duniya, da kofin zakarun turai, kuma yana da gogewa sosai.
Ya cigaba da cewa, tunda kungiyar ta Fatih Karagumruk ta samu nasarar shigowa babban rukunin gasar kasar, take son taga ta cigaba da samun nasara akan Galatasary, Trabzonspor da kuma Fernaberce.
Abikin Ahmed Musa yace kungiyar ta Fatih Karagumruk tana da tabbacin Ahmed Musa zai taimaka mata wajan samun nasara akan manyan kungiyoyin kwallon kafa ta kasar ya sanya suka sayeshi akan dala miliyan 2.5 da kuma sauran wadansu alawansi.
A wani labarin, AHMED MUSA: Dalili na na barin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
Dan wasa Ahmed Musa, yabar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bayan share watanni uku, inda ya koma wata kungiyar kwallon kafa ta Fatih Karagumruk dake Kasar Turkiyya.
Adai ranar Alhamis ne Dan wasa Ahmed Musa ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk har na tsawo shekaru biyu bisa Yarjejeniyar kara shekaru nan gaba.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk yace ” na yi sha’awar zuwan kungiyar ta Fatih Karagumruk ne saboda kudirin su, da kuma kyakykyawan manufarsu.”
Ya cigaba da cewa ya shirya tsaf don ganin sauran abokanan wasan sa, su zo don su cigaba da baiwa Fatih Karagumruk gudummawa da iya karfin sa.
Kungiyar dai ta Fatih Karagumruk ta samu nasarar dawo wa babban rukunin kwallo na Kasar Turkiyya a kakar wasa ta 2019-2020 bayan ta share shekaru 35 ta neman haka.
Kungiyar ta Fatih Karagumruk suna cigaba da shirye-shiryen su inda za suyi wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta Alanyaspor da Kasimpasa a ranar July 30 da August 5.