By Abbas Yakubu Yaura
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG) Don Awunah ya rasu.
Binciken da wakilinmu ya samu ya nuna cewa marigayi AIG Don Awunah, haifaffen jihar Benue, ya rasu ne a safiyar ranar Litinin bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, inda yake jinya.
Har zuwa rasuwarsa, Don Awunah ya kasance mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG).
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumiyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar wa wakilinmu rasuwarsa, ya ce ya rasu ne a safiyar ranar Litinin.
A cewar wata majiya mai tushe, za a bayyana shirye-shiryen binne shi nan gaba kadan.
A wani labarin kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin coci a jihar Ondo
Jaridar Blueprint ta rawaito cewa dansa da ke tare da shi a lokacin da lamarin ya faru, shi ma ‘yan bindigar sun yi garkuwa da shi.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda lamarin ya rutsa da su na tafiya a kan titin ne ‘yan bindigar suka tilasta wa motar su tsayawa, inda suka ja su cikin daji.
An kuma tattaro daga wata majiya cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Venerable Obanla, inda suka bukaci a ba su kudi naira miliyan 10 domin a sako mutanen.
An ce iyalan sun yi nasarar tara Naira miliyan 1 kamar yadda aka ruwaito a lokacin da aka bayyana hakan, wanda ‘yan bindigar suka yi watsi da shi gaba daya.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce ana ci gaba da kokarin ceto wadanda lamarin ya shafa.