Wata Kotun Majestire dake da zama a Kaduna garin Gwamna ta garkame wani matashi dan kimanin shekara 30 mai suna Auwal Suleiman a gidan yari bisa laifin yiwa wata matashiya yar Shekara 20 fyade.
Babbar Majestire Hajara Dauda wacce ta ki karɓar rokon Auwal ta umarci yan sanda da su karkato da akalar takardar Shari’ar zuwa gaban Babban Daraktan Kula da Kararraki na Jihar Kaduna don daukar matakin da ya dace.
Kuma tuni Majestire Hajara Dauda ta dage karar wanda yan sanda suka shigar gaban ta izuwa ranar 19 ga watan Afirelun 2021.
Tun Farko Lauyan Mai shigar da kara Sufeta Sunday Baba ya bayyana wa Kotun cewa Auwal wanda asalin sa mazaunin garin Rigasa ne ya yi wa matashiyar ne fyade a ranar 12 ga watan Maris wuraren karfe uku na yammaci.