Babban Daraktan bangaren Gas da Wutar Lantarki na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mista Abdulkadir Ahmad, a jiya Talata, ya ce Aikin bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKKP) ya kai kashi 73.3 bisa 100.
Gwamnatin Tarayya ta amince da aikin kwangilar jigilar iskar gas daga Ajaokuta, dake jihar Kogi zuwa ya biyo ta Jihar Kaduna, zuwa jihar Kano.
Mista Ahmed ya bayyana haka ne a wajen laccar da kungiyar Injiniyoyi masu sinadarai ta kasa (NSCHE) reshen Kaduna ta shirya da nufin karrama Sarkin Lere a Jihar Kaduna, Suleiman Umaru.
Ahmad, wanda Babban Manaja, Kamfanin Gas na NNPC, Emmanuel Ibokwuwe, ya wakilta, ya yi jawabi a kan: “Mai tsare-tsaren iskar gas na Najeriya da damammaki ga jihohin Arewa.”
Ya ce: “Ya zuwa yanzu mun samu gagarumin ci gaba domin aikin ya kai kusan kashi 73.3 bisa dari, kuma kashi 23.5 ne kawai ya rage.
“Mun raba aikin gida biyu don tabbatar da cewa an kammala shi a farkon lokacin da muke aiki a cikin wa’adin 2022.”