Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya mayar da martani ga gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, game da ikirarin da ya yi cewa bankin koli ya buga karin Naira biliyan 50 zuwa biliyan 60 don cike kason jihohi.
Emefiele ya kara da cewa “abin takaici ne kuma bai dace ba” ga wasu mutane su baiwa wannan batun wata fassara ta daban har ma su riƙa yaɗawa.
“Idan kun fahimci manufar buga kudi. Batun buga kudi shine batun bada bashi. Wannan aikinmu ne Don haka babu buƙatar sanya takaddama game da hakan kamar yadda na hangi wasu a gefe suna yi.