Gwamnatin Tarayya tana wani ƙoƙari domin karɓar bashi daga Turai, sakamakon tsaiko da aka samu a Ƙasar China.
Bashin da za’a amso a China za’a yi amfani dashi, wajen aikin hanyar jirgin Ƙasa a matsayin wani babbar Nasara a Gwamnati maici a yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar APC a Landan ta buƙaci a ɗage Zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na ranar 26 ga watan Fabrairu
A farkon satin nan, rahotanni da suka fito daga Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewar Najeriya na fuskantar matsaloli wajen karɓo bashi daga China.
A lokacin da aka tambaye shi akan tabbacin rahoton, bayan taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa Amaechi ya bayyana cewar “gaskiya shiyasa akwai tsaiko. Muna jiran Kasar China ta bamu bashin da muka nema, har yanzu basu maido mana amsa ba. Suna ta kawo tsaiko, kila zai kai ƙarshen wa’adin mulkin mu ba. Munje Bankin Ƙwararru, bayan sunyi dubi, sun amince a bamu wasu kuɗin.
“Muna neman Bankin Ƙwararru na Standard Chartered daya bamu bashi domin gina hanyar jirgin Ƙasa ta Lagos-Kano, kuma daga ciki, wasu kuɗin zasu zo daga wani bankin kuɗi a China.”
A lokacin da aka tambaye shi, sanin adadin kuɗaɗen da zasu karɓo daga Europe, yace “banda adadin a kaina, dole sai naje ofis.