Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga shugabannin Arewa da su yi koyi da takwarorinsu na Kudu maso Yamma wajen dora mata a matsayin mataimakan gwamnoni.
Ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan rikicin da ya barke a jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa.
KARANTA KUMA Aisha Buhari Na Kokwantan Ko Gwamnatinsu Ta Cimma Muradan Yan Najeriya
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda rikici ya barke a jihar bayan zaben fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar da Sanata Aishatu Binani ta lashe wanda daya daga cikin masu neman tsayawa takarar, Malam Nuhu Ribadu ya ki amincewa ya garzaya kotu.
A watan da ya gabata ne babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwani tare da bayyana jam’iyyar ba ta da dan takarar gwamna a jihar, lamarin da ya sa jam’iyyar APC da Binani suka kai karar kotun daukaka kara domin yanke hukunci.
Tuni dai lamarin ya raba kan jam’iyyar tsakanin mambobin da ke goyon bayan Binani da kuma masu goyon bayan Ribadu.
Amma wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, ta bayyana Binani a matsayin yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a Adamawa.
Da take yin la’akari da lamarin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Talatar nan, uwargidan shugaban kasar ta ce, “In sha Allahu, ina mika godiyata ga shugabannin jam’iyyar APC na jihar Adamawa bisa ziyarar ban girma da suka kawo min, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022.
A Wani Labarin Kuma Kotu Yankewa IGP, Usman Baba Hukuncin Zaman Gidan Yari
Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talatar nan ya yanke wa babban Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.
Mai shari’a Olajuwon wanda ya yanke hukuncin ya ce umarnin ya biyo bayan karar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Patrick Okoli ya shigar inda ya ce ya yi ritaya daga aikin ‘yan sandan kasar ba bisa ka’ida ba akan tilas.