Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta bada tallafin kayayyakin lafiya a wani mataki na yaki da cutar Korona.
Kakakin Uwargidan shugaban kasar, Aliyu Abdullahi, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Asabar a A Abuja, inda ya ce Dr Hajo Sani, mashawarciya kan harkokin mata, ita ce ta wakilci Aisha Buhari a yayin raba kayayyakin tallafin A Abuja.
Aisha Buhari ta nuna damuwarta bisa yadda cutar Korona ke yaduwa a sassan kasarnan, inda za ta yi amfani da shirinta na ‘Get Involved Initiative’ wajen tattaro masu son tallafawa wajen wannan yaki na Korona.
Ta mika godiyarta ga wadanda suka baya da gudummawar, ta kuma kara da cewa, al’umma kasar za su amfana da taimakon gaba daya.
Aisha Buhari ta bukaci al’ummar kasarnan su rungumi matakan kariya daga cutar ta hanyar rage shiga cunkoso da bibiyar shawarwarin likitoci don a samu nasarar dakile cutar daga Nijeriya.