Uwargidan shugaban Kasar nan Aisha Muhammadu Buhari ta shirya wata tawagar likitocin zuciya ta Future Assured da za ta shiga tsakani wajen rage yawan masu fama da cututtukan zuciya, wadanda suka dauki nauyin yi wa ‘yan Najeriya.
Tawagar, wacce ta dauki wasu kwararrun likitocin bugun zuciya daga Italiya, za ta hada da likitocin Najeriya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, a Jabi, da ke Abuja.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Da take jawabi yayin liyafar maraba, Misis Buhari ta ja hankali kan yadda cututtukan zuciya ke karuwa a tsakanin ‘yan Najeriya, lamarin da ta kara da cewa, yana da tsada sosai ga talakawan Najeriya da ba za su iya magance su ba, wanda ke haifar da cutuwa da mace-mace.
KU KARANTA KUMA Aisha Buhari Ta Janye Karar Da Ta Shigar Da Wani Dalibin Jami’a
Ta bayyana kwarin gwiwar cewa hadin gwiwa tsakanin likitocin kasashen waje da na cikin gida zai haifar da canja wurin kwarewa da kuma ceton rayuka da dama.
Hajiya Aisha a cikin wata sanarwa da kakakinta Suleiman Haruna ya fitar a ranar Talata, ta yi kira ga masu hannu da shuni da su samar da kudade don daukar nauyin jinya masu tsada kasamcewar tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya marasa galihu.
Babban daraktan kula da lafiya na cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Jabi, Farfesa Saad Ahmed, ya bayyana farin cikinsa da zabin asibitin da ta zaba domin gudanar da aikin tiyatar, inda ya kara da cewa a matsayinsu na asibitin gwamnati mafi kyau a kasashe rainon Burtaniya, an san su da gudanar da irin wadannan ayyuka da dama kuma masu kyau yanzu.
Ya kuma yabawa uwargidan shugaban kasar bisa samar da na’ura ta zamani mai suna Quantum Medtronic Heart Lung Machine tare da na’urar gano cutar, wanda ake bukata domin gudanar da aikin tiyata irin wannan.
Wannan na’ura, in ji shi, ita ce ta farko da aka kera ta a yankin kudu da hamadar Sahara.
A Wani Labarin Kuma Babu Wani Takameman Adadin ‘Yan Nijeriya Da Suka Bata – Gwamnatin Tarayya
Ministar Agaji da jin kai da kula iftila’i da Ci gaban Jama’a, Sadiya Umar-Farouk, ta ce babu wani sahihin bayanan kasa kan adadin mutanen da suka bace a Najeriya saboda babu wata rajista a hukumance.
Ta bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatarta ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) da kuma hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC).