Uwargidan shugaban kasa Buhari, wato A’isha Buhari ta gargadi ‘yan Nijeriya da su guji yada labaran karya a shafukan sada zumunta. A’isha Buhari ta nemi hakan ne jim kadan da saukarta Nijeriya daga kasar Birtaniya a filin sauka da tashi na Nnamdi Azikwe dake Abuja da safiyar ranar Lahadi.
Matar gwamnan Kogi, Rashida Bello, da Dr Hajo Sani da matar tsohon gwamnan Nasarawa, Mairo Al-Makura da sauran su suna daga cikin wadanda suka tarbe ta a filin jirgin.
Sannan ta bayyana jindadinta bisa wannan tafiyar da ta yi ta kuma dawo Nijeriya lafiya. Inda ta ce ta yi tafiyar bisa shawarar Likitanta.
Har wala yau A’isha Buhari ta jaddada cewa; yada labaran karya ba abu ne mai kyau ba, a don haka ta yi kira ga hukumomin da suka dace da su dauki matakan da suka dace. Ta ce idan har aka bari ana ci gaba da yada labaran karya, kasarnan za ta fada wani irin yanayi mara dadi.
Ta yi tilawar yadda tun lokacin da mijinta ya yi fama da rashin lafiya ake yada labaran karya. Inda