Uwargidar Shugaban Kasar Nijeriya, Hajiya Aisha Buhari ta yi kira ga ‘yan Afirka da su canza tunani kan tsagwamar mata marasa haihuwa.
Aisha Buhari ta yi wannan bayani a wata takarda da mai taimaka mata a kan harkokin yada labarai, Aliyu Abdullahi ya fitar. Bayanin nata ta yi shi ne a wurin tattaunawar da kwamitin Uwayen gidan shugabannin kasashe suka gabatar kan maudu’in “Building Healthcare Capacity” on the African continent.
Taron shi ne irinsa karo na shida wanda aka shiryawa uwayen gidan shugabannin Afirka, wanda na wannan karon aka gudanar a Accra ta kasar Ghana, bisa jagorancin Uwargidan Shugaban Kasar, wato Madam Rebecca Akufo-Addo.
Aisha Buhari ta ce; “ina son yin amfani da wannan damar wurin kira ga al’ummar Afirka da su sauya tunaninsu na kallon mata marasa haihuwa a matsayin wasu masu fama da matsala.”