Matar shugaba Muhammad Buhari a ranar asabar zata gana da matan Najeriya Dan gane da sabon shafi mai zuwa.
Ganawar zata bada gudunmuwa yadda mata zasu bada gudunmuwa a siyasa da kuma lafiya ga rayuwar su.
Hakan ya fito ne ranar alhamis daga bakin Hajiya Mariya Rufa’i ,sakatariyar karamin kwamitin da matar shugaban kasa ta saka kan bikin rantsuwa a Abuja.
Tace Aisha buhari zata karbi bakuncin yara inda za a shirya musu kwarya kwaryar liyafa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Matar shugaban duk tana hakan ne Dan kara habaka rayuwar mata da yara kan lafiya a kasar nam.
Cikin abinda zata gabatar sun hada da ilimin mata,ilimin matasa da koyar da su sana’oi da kuma wayar da kan mata kan harkar shaye shaye.