Matar Shugaban ƙasa Aisha Muhammadu Buhari ta tafi Dubai neman, magani, kamar yadda bayanai suka bayyana.
Kamfanin dillancin labarai ya gano cewa ko a ƙarshen makon jiya sai da Aishan Buhari ta fita zuwa ƙasar waje saboda ciwon wuya da ya takura mata jim kaɗan bayan dawowarta Abuja daga Legas.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ta fara fama da ciwon wuyan ne tun kusan lokacin da ta dawo daga ta’aziyyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, wanda cutar coronavirus ta yi ajalinsa.
Aisha dai ta killace kanta na tsawon makonni biyu bayan ciwon wuyan nata ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kusan wata ɗaya da zuwa ta’aziyyar a Legas.
https://dimokuradiyya.com.ng/aisha-buhari-ta-bada-tallafin-don-yaki-da-korona/
Hakan ne ya tilasta mata yanke shawarar zuwa Dubai don neman kulawar gaggawa.
Yanzu haka tana can a wani asibitin da ba a bayyana sunan ba, kuma tana samun saunƙi.
Da aka tuntubi hadimin matar shugaban ƙasar ta ɓangaren watsa labarai Barista Aliyu Abdullahi bai ce komai ba dangane da lamarin.