Akalla fasinjoji 41 ne suka mutu bayan wani jirgin saman Rasha ya yi saukar gaggawa kuma ya kama da wuta a filin jirgin saman Sheremetyevo da ke birnin Moscow.
Rahotanni da dama sun nuna fasinjoji na saukar gaggawa don kubuta daga cikin jirgin saman Aeroflot lokacin da ya tsaya yana cin wuta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai kananan yara biyu da wani ma’aikacin jirgi a cikin wadanda suka rasu.