Akalla Jagorori 50 aka koyar kan yadda zasu shawo kan matsalar cin mutunci mata da yara a Sokoto. Jaridar Tvcnews ta ruwaito
A yunkurin da akeyi wajan fada da cin zarafin mata da yara kanana a Sokoto, an gabatar da taro don ilimantar da jagororin al’umma na bangare daban-daban sama da hamsin kan yadda zasu kawo karshen matsalar.
KARANTA:- Yan gasar tsere na Najeriya sun kafa tarihi
Shuwagabanin al’umma da aka dorama alhakin yaki da cin zarafin mata da yara kanana an kuma kara musu da ilimin kan yadda zasu kare mutanen su da kamuwa da cutar Covid-19.
Wadanda aka baiwa ilimin sun hada da sarakunan gargajiya da malaman addinai da jagororin matasa.
Sun fito daga yankin Sokoto ta Yamma daga Karamar Hukuma Dange da Shuni inda duk a basu tsari yadda zasu shawo kan matsalar cin zarafin mata da yara kanana.
Kungiyar UNPFA (United Nation Population Fund) da PPFN (Plan Parenthood Federation of Nigeria) da kuma wata Kungiya mai zaman kanta suka dau nauyin gudanar da taron.
Hafsatu Halilu Jagoran PPFN ta Jahar tace an gudanar da taron ne don ilimantar da jagororin al’umma na kowane Karamar Hukuma ta yadda zasuyi magani matsalolin.
Tace daman wannan shine kudurin taron.
Tace hakan kuma zai cigaba har zuwa sauran kananan hukumomin ashirin da daya dake jahar.
Ibrahim Galadanci Shugaban Kungiyar ya e taron zai taimaka sosai wajan kawo cigaba ga sarakunan da kuma yankin su.
Yace zakuma a cigaba da baiwa sarakunan da kuma jagorori ilimi akan hakan domin cin nasara akan kawo karshen cin zarafin mata da yara kanana.