By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 12 ne suka kone kurmus a wani hatsarin mota da ya afku a garin Tsamawa dake karamar hukumar Garun Malam a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Talata a Kano.
“Mun samu kira daga wani mai suna Isah Mai-Fetur da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin cewa wata motar bas kirar Hiace da wata motar bas J5 sun yi karo da juna inda kuma wuta ta tashi nan take.
“Bayan samun labarin, mun aika da tawagarmu da gaggawa zuwa wurin da abin ya faru inda suka isa wurin da misalin karfe 3:12 na rana domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.
Ya ce mutane 11 da ke cikin motar Hiace sun taho ne daga hanyar Zariya zuwa Kano, yayin da mutum daya a cikin motar J5-bus shi ma yake kan hanyar Kano zuwa Zariya ta jihar Kaduna.
Abdullahi ya ce dukkan mutanen 12 sun kone kurmus, kamar yadda ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri.
Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika tuka mota a hankali domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.