By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane shida ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota daya afku a yankin Tungan Maje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Kazalika, an ce mutane tara ne suka jikkata a hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 10 na safiyar ranar Juma’a.
Wani ganau wanda ya bayyana sunansa da Austin ya ce hatsarin ya faru ne a sanadiyyar wata babbar mota da direbanta ya rasa yadda zai yi, daga bisani kuma ya kutsa cikin wata motar kasuwanci yayi awon gaba da ita.
Ya kara da cewa mutane biyar ne suka mutu nan take yayin da wani fasinja ya mutu a kan hanyar zuwa asibiti, inda ya ce uku sun tsira ba tare da jikkata ba.
Ya ce, “Hatsarin ya yi muni sosai kuma wurin ya kasance mai ban tsoro. Ya hada da motar kasuwanci da babbar mota. Motar ta yi gudu da sauri kafin ta kutsa cikin motar kasuwanci.
“Da farko biyar sun mutu nan take amma daya daga cikin wadanda suka jikkata ya mutu a hanyarsu ta zuwa asibiti. Mutane uku ne suka yi sa’a, sun fito ba tare da jin rauni ba. Jami’an hukumar kiyaye hadurra ta tarayya sun zo domin garzayawa da su zuwa asibiti. Tuni dai suka kwashe tarkacen motocin dake kan hanyar”
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa na FCT, Ogar Ochi, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya kara da cewa wuce gona da iri ne ya haddasa shi.
Sannan ya ce, “Mutane 18 ne suka yi hatsarin. An tabbatar da mutuwar mutane shida, yayin da wasu tara suka jikkata. Hadarin ya afku ne sakamakon wuce gona da iri.”