By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyu ne suka mutu tare da jikkata wasu 22 a ranar Alhamis sakamakon wani harin bam da aka kai a wata unguwa mai cike da hada-hadar kasuwanci da ke birnin Lahore na Pakistan, in ji jami’an ‘yan sanda.
“Bincike na farko ya nuna cewa na’urar da take kayyade lokaci ce a kan babur wadda ita ce musabbabin fashewar,” Rana Arif, kakakin ‘yan sandan Lahore, ya shaida wa AFP.
Majiyoyin asibiti da ‘yan sanda sun ce mutane biyu ne suka mutu – ciki har da wani yaro – sannan 22 suka jikkata a fashewar, wanda ya faru a tsohuwar gundumar Lahore mai cike da hada-hadar kasuwanci ta Anarkali.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma ana ta samun hare-haren bama-bamai da kai hare-hare kan jami’an ‘yan sanda tun cikin watan Disamba lokacin da aka samu sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan Taliban na Pakistan.
Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) – wata kungiya ce ta gida wacce ke da tushe daya da kungiyar Taliban ta Afganistan – ta sha daukar alhakin mafi yawan wadannan abubuwan.AFP