Hukumar ‘yan Sandan kasa da kasa ta Interpol ta samu nasarar ceto akala mutum dari biyar da ake bautar da su ko ake kan hanyar sayar da su ga masu fatauci don isa da su wasu kasashe daban.
‘Yan Sanda a wannan aiki da suka kaddamar da shi tun a ranar 28 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu da kuma suka yiwa sunan Weka da yaren Swahili, manufa tsaya ta shafi kasashe 24 a duniyar nan.
Daga cikin kasashen da ‘yan sanda suka kai wannan samame za mu iya zama Afrika ta kudu, Kenya, Sudan, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Morocco, Tunisiya, Sipaniya da Girka.
A Afrika ta kudu, ‘yan Sanda sun kama ‘yan kasar Chana biyar dake aiki karkashin wata masaka da kuma ke amfani da ma’aikata ba bisa ka’aida ba.