By Abbas Yakubu Yaura
Fiye da yara 20 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wata gobara data tashi a wata makaranta a birnin na biyu mafi girma a Jamhuriyar Nijar da safiyar ranar Litinin, a cewar hukumomi a Maradi.
Gobarar ta cinye azuzuwan makaranta guda uku da aka yi da bambaro, inda ta kashe yara ‘yan tsakanin shekara uku zuwa takwas, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
Ba a dai san musabbabin tashin gobarar da kuma inda ta taso ba, kuma an fara gudanar da bincike, kamar yadda hukumar kula da ilimi ta yankin ta tabbatar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Akan yi amfani da bukkokin bambaro wajen bawa dalibai daki a makarantu masu cunkoso a Nijar.sannan A cikin watan Afrilu ne wata gobara data tashi a wata makarantar firamare dake wajen Yamai babban birnin Nijar, inda ta kashe yara 20.
Tun daga wannan lokacin ne malamai da iyayen yara suka ce mutuwar ta na nuni da illar dakunan karatu na wucin gadi da aka kafa a waje.