By Abbas Yakubu Yaura
Ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godwill Akpabio, ya ziyarci jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, kan rugujewar wani bene mai hawa 21 a yankin Ikoyi dake jihar Legas.
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a shafinsa na sada zumuntar Facebook da aka tabbatar, inda ya yada hoton kansa da Tinubu.
Ya rubuta cewa, “Na kasance a gidan jagoran babbar jam’iyyar mu, Asiwaju Ahmed Tinubu, a ziyarar jajen rugujewar ginin data faru a Legas, inda ‘yan Najeriya da dama suka rasa rayukansu.
“Na yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu a cikin wannan mummunan lamari. Na kuma yi amfani da wannan ziyarar wajen maraba daga dawowar shugaban namu daga ziyarar jinya da ya yi a kasar waje tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya a yalwace.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rushewar ginin Ikoyi wanda ya faru a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2021, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40 tare da jikkata wasu da dama.
Comments 1