By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa, wani kuma ya samu rauni a wani hatsarin mota da ya afku a ranar Litinin a kan hanyar IBB, kusa da Cibiyar Raya Mata a Uyo.
Hadarin ya rutsa da wata motar Mack ta kamfanin gine-gine na AMITEC mai lamba KPR321XA da kuma babur mai kafa uku KVS King mai lamba JW740KET.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Matthew Olonisaye shine ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata ya alakanta musabbabin hatsarin da fashewar birki.
Kazalika ya shawarci masu ababan hawa dasu dinga kula da ababen hawan nasu da muhimmanci, ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yiwa masu ababen hawan sulhu a kan hakan.
“Bai kamata masu ababen hawa su dauki lafiyar ababen hawansu da wasa ba. Rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da daukar mataki akan motocin da ba su dace ba. Ya kamata masu amfani da hanyar su bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa kuma su ci gaba da ba jami’anmu hadin kai don rage tabarbarewar hanyoyin,” in ji Olonisaye.
Comments 1