Majalisar Dinkin Duniya tace akwai fargabar mummunan bala’i na kare hakkin dan adam a Myanmar yayin rahotannin ke cewa dubban sojoji na taruwa a yankin arewacin kasar dake kudu maso gabashin Asiya, wacce ke cikin rudani tun bayan juyin mulkin watan Fabrairu.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan Myanmar Tom Andrews, yace ya zama wajibi su kasance cikin shiri, kamar yadda hukumomin Myanmar ke tsara shirin aikata manyan laifuka na kisan gilla.
Fiye da fararen hula 1,100 ne aka kashe a rikicin kasar yayin da aka kame sama da mutane dubu 8 a kokarin sojoji na murkushe ‘yan adawa tun bayan juyin mulkin, kamar yadda alkaluman wata kungiyar dake sa ido ta cikin gida ya nuna.
Andrews, wanda ke gabatar da sakamakon rahoton kare hakkin dan adam na shekara -shekara kan Myanmar ga Babban Taron, Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ya sami labarin cewa ana tura dubban sojoji da manyan makamai zuwa yankuna masu fama da tashin hankali a arewa da arewa maso yamma.