Shugaban hukumar Kwastam ta Nijeriya, Kanal Hameed Ali (mai ritaya), a ranar Alhamis ya shaidawa masu safarar kaya zuwa Nijeriya cewa su fitar da bata-gari a cikinsu a tasoshin da ake shigo da kaya gida Nijeriya.
Hameed Ali ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin kungiyar ‘yan Nijeriya masu lasisin daga Kwastam, ANLCA bisa jagorancin Iju Nwabunike a birnin tarayya Abuja.
Hameed Ali ya ce ba shakka akwai gurbatattu daga masu shigo da kaya cikin kasa, kuma ya zama dole a fitar da irin wadannan gurbatattu din daga cikin jami’an Kwastam da kuma masu wakiltar su.
Shugaban Kwastam din ya nuna muhimmancin yaki da masu rashawa a cikin al’amarin domin amfanar kasa baki daya. Hameed Ali ya ce bai dace ba masu ruwa da tsaki a al’amuran su zuba ido su bar wadansu gurbatattu suna yin yadda suka ga dama.
Inda ya shawarci masu shigo da kayan da su yi azamar watsi da irin wadannan bata-gari, tare da kuma bin ka’idojin da aka gindaya na shigo da kayayyaki ta tasoshin Nijeriya.