Wani shahararren mai fashin baki, Mista Ifeanyi Olumba ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da tallan magungunan batsa da masu sayar da maganin gargajiya suke yi a bakin hanya. Kamar yadda shafin yada labarai na Tantabara Hausa ya labarto.
Masanin ya ce, wannan abin da suke yi damfara ne da yaudarar mutane, domin mafi yawan magungunan nasu na bogi ne. Ga su kuma da qwarewa wurin kalaman janyo hankalin al’umma.
Olumba wanda lauya ne, ya yi wannan kira ne yau a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya.
Ya ce, baya ga yaudara da karairayin da ke cikin bayanan nasu, akwai kuma illa ga tarbiya da kalaman batsan da suke yi yake yi ga qananan yara.