Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wato Aisha Buhari ta yi kira ga masu ruwa da tsaki musamman Iyaye da su tabbata suna ciyar da ‘ya’yansu da abinci mai gina jiki domi bunkasa lafiyarsu.
Aisha Buhari ta ba da wannan shawarar ne a jiya Alhamis a Abuja ta hanyar shafinta na sada zumunta. Aisha Buhari ta tabbatar da cewa; bincike ya nuna cewa a cikin kowanne yara kanana guda uku ‘yan kasa da shekara biyar a Nijeriya, akwai guda daya daga ciki da yake fama da matsalar abinci mai gina garkuwar jiki.
Inda ta ce; “Bai wa ‘ya’yanmu abincin da ya dace mai gina jiki, zai bunkasa lafiyar ‘ya’yanmu da ma girman halittarsu, wanda wannan yana da muhimmanci, kuma al’amari ne da ya kamata a ce kowa ya aikata shi.” In ji ta.
Ta kara da cewa; akwai bukatar a hada hannu da karfe wajen yakar rashin abinci mai gina garkuwar jiki. Inda ta nemi ganin ta yaki wannan lamarin.