Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai bukatar a dauki kwakkwaran matakai kan masu cin zarafin mata a makarantun dake fadin kasarnan.
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Juma’a. Inda ya ce Buhari na maida martanin nan ne bayan bidiyon fallasan da aka fitar dangane da yadda wadansu Malaman Jami’a s’ke neman yin lalata da wadansu dalibansu mata.
Ya bayyana kuma jindadinsa kan yadda binciken fallasan da BBC suka yi na bankado wadansu Malaman Jami’ar jihar Legas kan yadda suke neman lalata da dalibansu mata. Inda ya bukaci zai yi tabbatar kwakkwaran mataki a dokance musamman duba da hakan da majalisar ta mika masa.
Shugaba Buhari ya ce wannan dokar da majalisar ta mika masa, za ta samu goyon bayansa musamman ma idan dokar ta dace da dokokin Nijeriya, in ji shugaban kasar.