Kungiyar ‘National Association of Seadogs (NAS),’ ta shawarci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar yiwa ‘yan gudun hijira rijista domin tantancewa da duba yiwuwar ganin gwamnatin ta fadada tallafin da take ba su zuwa ga saura wadansu wuraren ‘yan gudun hijirar musamman da gwamnatin tarayya ba ta musu riista ba.
Daya daga cikin memban kungiyar, Sahara Deck, shi ne ya yi wannan kiran a yayin bai wa ‘yan gudun hijirar tallafin magani a New Kuchingoro a Abuja.
Dr Joseph Oteri, wani jami’in lafiya da kungiyar, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dauki matakin da suka dace wajen magance matsalolin da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta.
Oteri ya jaddada cewa; akwai bukatar dukkanin taimakon da gwamnatin tarayya za ta bai wa wadansu ‘yan gudun hijirar da suke zaune a sansanonin da aka samar musu a Arewa maso gabashin kasarnan, a mika irin wannan tallafin ga sauran ‘yan gudun hijirar a sassan kasarnan.