Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi gargadin cewa matakin da kasashe suke dauka na fesa magani a saman tituna da kasuwanni da ma kan mutane da a wani mataki na kashe kwayoyin cutar Korona babban hadari ne ga lafiyar jama’a.
A wani littafi da ta wallafa a ranar Asabar kan muhimmanci tsarkake wurare da nufin kashe kwayoyin cutar Korona, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce babu tabbacin cewa yadda ake bada maganin na yin tasiri wajen kashe kwayoyin cutar wacce ya zuwa yanzu ta kashe mutane sama da dubu 300 a duniya.
Hakazalika hukumar ta ce tituna ba nan ne matattarar kwayoyin cutar ba, sannan magungunan da ake fesawa wadanda na Kemestri ne na da hadari ga lafiyar Dan Adam, kuma ba sa hana mutumin da ya harbi da cutar ya ci gaba da yada ta ga jama’a ta hanyar dafawa ko tsattsafar yawun da ke fita daga bakinsa a lokacin magana kamar yadda rahoton DW Hausa ya tabbatar.