Kwamanda-Janar na Hukumar jami’an tsaron Farin kaya ta sibil difens na ƙasa Dr Ahmed Audi, ya alaƙan yaɗuwar ta’addanci da aikace ƴan ta’adda a ƙasar, ga masu bada bayanan sirri a cikin Hukumomin tsaro da kuma al’umma.
Ya yi kira da’a shigo da al’ummomi, da shuwagabannin addini, dana siyasa, domin magance matsalolin tsaro dake yaɗuwa a ƙasar, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
Dayake jawabi a taron masu ruwa da tsaki akan ma’adanai na ƙasa, da gine-gine a cibiyar Rundunar Sojin sama dake Abuja a ranar Talata, ya jaddada buƙatar dake akwai da aƙara ƙaimi domin kula da ma’adanan ƙasar ga ɓata gari a cikin al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari ya amince da Bai wa Gidajen Rediyo da Talbijin 159 Lasisi a Nigeria
A cewar sa, ƙaruwar ta’addanci a ƙasar yana haifar ƙalubale ga ma’adanan ƙasar da gine-ginen gwamnati, kamar yadda ake gani a wasu jahohi da suka haɗa da Zamfara, da Kaduna, da Borno da wasu jahohi a arewa.
Ya bada misali da jawabin Ministan yaɗa labarai Lai Mohammed, wanda ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na kashe Naira Biliyan 60 akan gyara da kula da bututun mai a faɗin ƙasar.
Yace “zaku yarda dani cewa, aikace-aikacen waɗannan ƴan ta’adda ana bashi kula ta musamman bawai ga masu bada bayanan sirri ba a cikin jami’an tsaro, harda al’umma, don haka akwai buƙatar shigo da masu riƙe da sarautun gargajiya, da shuwagabannin siyasa, da shuwagabannin matasa, wajen gano wannan matsaloli.”
Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, yayi nuni dacewar, ƙalubale dake tunkarar ma’adanan ƙasa da gine-ginen gwamnati, shiya haifar da matsalar tsaro a ƙasar.
Comments 1