Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya yarda cewa akwai wasu bakaken Aljanu a cikin gidan gwamnatin jihar. Gwamnan ya bayyana wannan ne a Yau, 2 ga Watan Nuwamba.
Gwamna Willie Obiano ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron addu’o’i da aka shiryawa jihar ta Anambra. Mabiya Anglikan ne su ka shirya wannan taro da aka yi wa lakabi da APRAS 2019. Obiano ya yi wannan jawabi ne ta bakin Sakataren gwamnatin jihar Anambra, Farfesa Solo Chukwubelu.
An gudanat da taron ne a babban filin Dr. Alex Ekwueme da ke babban birnin Awka. Gwamnan ya yi magana ne bayan abin da babban Faston Darikar na Angilika, Bishof Prosper Amah, ya fada. Malamin addinin ya tabbatar da cewa akwai Ifiritai a gidan gwamnatin Anambra.