Fitacciyar wacce take kiran kanta yar gwagwamayar nan a Najeriya Aisha Yessufu ta ce babu abinda zai sanya ta hada lambae katin dan kasarta da kuma lambar waya kamar yadda Gwamnati ta bukata.
Cewar ta yin hakan ka iya damka duk wasu bayanan ta wa mai jinkan yan ta’adda da ma su kansu yan ta’addan.
Wannan jawabi dai nata kai tsaye na zuwa kan Ministan Harkokin Sadarwa da Bunƙasa tattalin arziki Fasahar Zamani NITDA wato Isah Ali Pantami, wanda shine kanwar uwar gamin kirkiro da wannan sabon tsari, duk da cewa ba bakon al’amari ba ne a ƙasashen duniya da suka ci gaba.
Wani wa’azin da Pantami ya gudanar shekaru 20 da suka gabata sun nuna yadda yake tausaya wa Ƙungiyar alkaida inda har ta kai ga an bukaci gwamnatin tarayya da ta tunbuke shi a muƙaminsa.
To sai dai gwamnatin tarayya ta sanya kafa ta shure kiraye-kirayen tsigen shi inda aka alakanta lamarin nashi da tashen kuruciya.