Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace akwai wani Ɗan Majalisar Dokoki ta Ƙasa dage cikin masu ɗaukar nauyin Igboho da Kanu, wanda so suke suga Nigeria ta rabe biyu.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka a jawabin da ya yiwa ƴan ƙasar, a ranar 1 ga watan Oktoba na Shekarar 2021, domin bikin murnar samun ƴancin kai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Dakatar Da Taron Wakilan NUJ
Yace shekaru 61 da samun ƴancin kai, bawai zai zama ya tunatar da ranar da turawa suka miƙa ragamar shugabanci, da ƴan Najeriya ba, a’a sai dai don an haɗa kan dukkanin ƙabilu da addinai gami da yankuna.
Yace dukkanin kowa yayi ƙoƙari domin ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960, domin ganin yankin Gabas da yamma da Arewa suzo su haɗa kansu don samun ƴancin kai.
Akan kama Nnamdi Kanu da Igboho, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace a binciken da ake cigaba da gudanar wa ya nuna cewa, akwai wasu manyan mutane da suke ɗaukar nauyin su.
“Muna kuma tuhumar masu ɗaukar nauyin su, ciki harda wani ɗan majalisa na ƙasa.
“Wannan ya nuna yadda misalin yadda mutane ke ƙyale matsayin su domin samun wani abu nason zuciya. Mai makon wa’azi akan zaman lafiya, suna ɗaukar nauyin su domin sanya matasan mu su gudanar da ta’addanci, wanda hakan ka’iya haifar da rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Kuma waɗannan shuwagabannin marassa kishi, da wani abu ya faru guduwa zasu yi zuwa ƙasar waje, a bar matasan mu da basu san komai ba, suje su cigaba da faɗace-faɗace da janyo lalata dukiyoyi.
muhammadumamuda689@gmail.com tudun nufawa kano Municipal local government area my market si kofar ruwa layi yantaya