Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya zargi cewa akwai wasu yan siyasa a kasar nan, wadanda ke Amfana da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin Kudancin Najeriya.
Umahi ya bayyana wannan hasashen nasa ne yau yayin hira da shi, da wata kafar yada labarai tayi, dangane da harkokin siyasar sa.
Gwamnan dai an tattauna da shi ne matsayin na dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, wanda kuma yake bayyana irin fatan da yake da shi wajen samar da ci gaba idan har ya kai ga samun nasara.
Ya kuma ce matsawar yayi nasara matsalar tsaron da ake fama da ita, zai magance ta a kankanin lokaci, domin kuwa zai fara ne da yanki zuwa yanki.
A cewar Umahi batu na tsaro harka ce da kowa ke da ruwa da tsaki a ciki dan haka, zai hada hannu da duk masu ruwa da tsaki wajen magance ta a kankanin lokaci.
Ya kuma ce idan da tsaro ne ci gaba yake tabbata a ko’ina a duniya, a dan haka tsaron da ya kuduri aniyar samarwa zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya.