Yayin da ake sa ran fara wasannin kwallon kafa daban daban a kasa Ingila, akwai yiwuwar muguwar cutar nan ta korona ta jinkirta fara wasannin.
A ranar Asabar ne ake sa rana za buɗe gasar kofin kalubale ta Carabao, to sai dai bisa ga dukkan alamu dai yanayin wasannin share fage da aka yi ka iya zama wani dalili na dage dukkanin wasannin kwallon kafar ta Ingila.
Karawa tsakanin Bournemouth da Sheffield Wednesday ita ce ta farko a kakar bana, kuma za a yi ra ne gaban dubban yan kallo wanda rabon jama’a da ganin hakan tun watan Maris din bara.
Yaɗuwar cutar ta korona na ci gaba da kawo fargaba a zukatan jama’a duk da cewa cibiyar lafiya ta Birtaniya ta yi gargadin hakan ka iya shafa harka tamaula.
An dage wasannin sharar fagen shiga gasar kwallon kafa ta Ingila daban daban sakamakon barkewar cutar, yayin da a hannu guda kuma aka ɗage wasu Wasannin sakamakon rashin bada tazara da yan kallo ke yi.
Na baya bayan nan shine karawa tsakanin Manchester United da Preston yayin da karawar Norwich City ita ma lamarin ya shafa hakazalika an ɗage tafiyar Arsenal zuwa kasar Amurka yayin ita kuwa Newcastle ta yi rashin masu tsaron gidanta uku sakamakon killace au da aka yi.