Tokunbo Awolowo-Dosunmu, diyar dan rajin kishin kasa a Najeriya, Obafemi Awolowo, ta zargi yiwuwar juyawa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Ta yi zargin cewa akwai wani shiri na kawar da Tinubu a nada abokin takararsa, Kashim Shettima a matsayin shugaban kasa.
KARANTA ANAN: Hukumar NDLEA Ta Kama Wasu Asusun Ajiya Na Banki 600
Awolowo-Dosunmu ta yi ikirarin cewa za a iya kammala shirin nan da nan bayan an rantsar da shi a shekarar 2023.
Ta ce wadanda ke da wannan shirin za su yi amfani da yanayin lafiyar Tinubu.
Awolowo-Dosunmu ta yi kira ga Yarabawa da su daina son zuciya da kabilanci game da manyan ‘yan takara uku da ke neman kujerar shugaban kasa.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sake Duba Albashi Malaman Jami’o’i
Gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biyan karin albashin kashi 23.5 na dukkan malaman jami’o’in dake fadin tarayya, in ban da shehunan malaman jami’o’i, wanda za a sake dubasu tare da kara musu kashi 35 cikin 100.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi tawagar gwamnatin da ke cikin tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aiki kan sanya hannu kan duk wata yarjejeniya da gwamnati ba za ta iya aiwatar da ita ba.