Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Asiwaju Tinubu ya mika Fom din sa na son tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC ga hukumar zabe ta INEC.
Tinubu dai shine yayi nasarar zama ɗan takarar jam’iyyar, bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani daka gudanar a Abuja tsakaninsa da yan takara 14.
Jagoran jam’iyyar dai tun a ranar Laraba ya saka hannu kan Fom din takarar, tare da mika shi ga hukumar kwanaki biyu kafin wa’adin da INEC ta basu ya kare.
Wannan batu dai mai taimakawa Tinubun kan kafafen yada labarai Tunde Rahman ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.
To sai dan kan hakan mun sake tuntubar Tunde Rahman Amma yace bashi da cewa yanzu, amma a kira ce shi.
Daga cikin sunayen da Tinubun ya bayar domin zabar daya cikin su har da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Yanzu haka dai Masari na kan gaba cikin wadanda ake tunanin Tinubun zai dauka matsayin mataimaki.