Mai yiwuwa kungiyar Barcelona ta kulla yarjejeniya da tsohon mai horas da Tottenham Mauricio Pochettino a sabuwar kakar wasa.
Kwararan majiyoyi daga Spain kamar yadda jaridar ‘Daily Mail’ ta ruwaito, sun ce a halin yanzu shugabannin kungiyar ta Barcelona sun bayyana Pochettino a matsayin koci na farko da suke son maye gurbin mai ci Quique Setien.
Batun maye gurbin Setien da tsohon kocin Tottenham ya karfafa ne a makwannin baya bayan nan, sakamakon gaza jagorantar Barcelona da yayi wajen lashe kofin gasar La Liga.
Kafin Barcelona, kungiyoyin da suka nemi kulla yarjejeniya da Mauricio Pochettino a baya sun hada da Juventus, Monaco da kuma Newcastle United.