Rahotannin sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar samun taƙaddama tsakanin babban Sufeton ‘yan sanda, Alkali Baba Usman, da hukumar kula da jami’an yan sanda ta kasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa taƙaddamar saka iya faruwa baya wuce yunkurin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda.
Hukumar kula da jami’an ‘Yan sanda ta bude shafin daukar sabbin jami’an yan sanda aikin na shekara ta 2022 tare da sanya tallan daukar ma’aikata a cikin jaridun kasa.
KARANTA ANAN: Magoya Bayan Peter Obi Barazanar PDP da APC Ne – Fani Kayode
Sai dai a martanin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi kan wannan lamari, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan talla.
A wata sanarwa a ranar Litinin, ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce tallan daukan jami’an yan sandan ba ta da alaka da rundunar ‘yan sandan Najeriya, kuma ba ta dace da tsarin daukar ‘yan sanda ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya na son sanar da jama’a masu kishin kasa cewa ba ta fara daukar ‘yan sanda aiki a shekarar 2022 ba sabanin yadda aka buga a shafi na 21 na Jaridar Daily Sun ta ranar Alhamis din 11 ga watan Agusta, 2022.
Idan dai za a iya tunawa, tsohon Sifeton yan sanda Mohammed Adamu da Shugaban PSC, Alhaji Musiliu Smith sun yi takun-saka kan hukumar da doka ta ba da damar gudanar da aikin daukar ma’aikata.
Hukumar dai ta maka tsohon sufeton da rundunar a gaban kotu saboda gudanar da aikin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda 10,000 a shekarar 2019.
A wani labarin kuma: Tilas Ne Yan Najeriya Su Zabi Tinubu a 2023 – Omisore
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sen. Iyiola Omisore, a ranar Litinin, ya ce babu wani zabi ga yan Najeriya a zaben shugaban kasa, illa su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki Sanata Bola Tinubu.
Omisore ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da wasu shugabannin jam’iyyar a sakatariyar APC da ke Legas.