Dukkanin alamu sun bayyana a fili cewar akwai yiwwuwar nan gaba shahararren ɗan wasa Christiano Ronaldo ya kafa babban tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa amma tarihin ba wai a iya ƙasar ba kokuma a ƙungiyoyin ƙwallon
ƙafan da yake fafatawa wasa, a’a a dukkanin su wato ƙasar sa da kuma ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan .
Hakan baya rasa nasaba da yawan ƙwallaye da yake zazzagawa a raga duba da yadda ya wanke ƙasar Sweden a daren jiya kuma ya cimma tarihin jefa ƙwallaye sama da guda 100 a daren na jiya.
Babban tarihin da ake ganin zai iya kafawa a nan gaba shine ana ganin zai iya fin ko wanne ɗan wasa jefa ƙwallaye a duniyar
ƙwallon ƙafa inda ake ganin zai iya karya tarihin da magabansa a tarihi suka kafa.
Ga jerin yawan ƙwallaye da kuma adadin wasannin da manyan ‘yan wasa suka kafa inda wasu kuma suke takemusu baya a halin yanzu.
1. Bican ya jefa ƙwallaye756 daga wasanni 494 daya buga.
2. Pele ya jefa ƙwallaye 757 daga wasanni 815 daya fafata amma saidai ance ragewa Pele yawan ƙwallayensa akayi domin yaci ball tafi 1000 a tarihi.
3. Romario ya jefa ƙwallaye 749 daga wasanni 972 daya bugs.
4. Christiano Ronaldo ya jefa ƙwallaye 739 daga wasanni 1015 daya buga.
5. Puskas ya jefa ƙwallaye 705 daga wasanni 715 daya buga.
6. Leonel Messi ya jefa ƙwallaye 704 daga wasanni 869 daya buga.
7. Gerd Muller ya jefa ƙwallaye 673 daga wasanni 749 daya fafata.