Babu tabbacin shahararren ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles wanda yafi kowanne ɗan wasa tsada a nahiyar Afrika wato Victor Osinhem ya sami damar fafata wasannin sada zuzuncin da Najeriya zata kara guda biyu ba a watan Oktoba na shekarara 2020 da ake ciki.
Hakan ta faru ne bisa gwajin cutar Coronavirus da aka yiwa kusan dukkanin jerin ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli, hakan ta faru ne bayan da ita Napoli ta fafata wasan mako na biyu na gasar Serea A da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Genoa wasan da ƙungiyar Napoli ta sami nasara daci 6 da nema, ashe tun kafin wasan an sami ‘yan wasan Genoa guda 11 da kuma wasu muƙarrabai na ƙungiyar suna da cutar ta Covid 19.
Jin hakan dai ya sanya mahukuntan na Napoli suka yiwa kusan dukkanin ‘yan wasan nasu gwajin wannan cuta domin neman kariya da kuma gane jerin ‘yan wasan da suka kamu da cutar sai a killacesu zuwa wani lokaci.
Ita dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta buƙaci Genoa ta bata sunayen ‘yan wasan ƙungiyar da aka tabbatar sun kamu da wannan cutar inda aka ga akwai wani ɗanwasa guda ɗaya tilo ta aka tabbatar sunyi ido huɗu da kuma duk wata ma amala da Osinhem na yadda zai iya kamuwa da ita, wannan ɗanwasa shine Andrea Masiello amma kuma baya daga cikin jerin ‘yan wasan da suke da cutar ta Coronavirus.
Anasa ran sakamakon gwajin da aka yiwa ‘yan wasan na Napoli zai fito a daren ranar Laraba sannan kuma dukkanin ‘yan wasan zasu sake komawa wani gwajin a ranar Juma’a wato sabon wata mai kamawa kenan, a jerin ƙasashen da annobar cutar ta Coronavirus ta yiwa rusau harda ƙasar ta Italiya inda ta kama mutane da dama.
Victor Osinhem dai yazo ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli a kakar wasa ta bana inda suka sayeshi daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lille dake can ƙasar Faransa a farashi mafi tsada kuma farashin da ba a taɓa sayen wani ɗan wasan nahiyar Afrika ba tunda aka fara sayen ‘yan wasan nahiyar.
Najeriya dai zata fafata wasannin sada zumuntar guda biyu a Jacques Lemans Arena dake can ƙasar Austria a ranakun 9 da kuma 13 ga watan na Oktoba, wannan kuma zasu fafata wasannin sada zumuntar da ƙasashen nahiyar Afrika wato Tunisia da Algeria.
Idan dai an tabbatar da cewar Osinhem ya kamu da wannan cutar to babu makawa bazai buga wasannin sada zumuntar guda biyu ba kuma za a iya killace shi, Osinhem dai yana daga cikin ‘yan wasan da ake ganin babu kamarsu a ‘yan wasan gaban Najeriya a halin yanzu duba da yadda ludayinsa yake kan dawo.