Akwai yiwwuwar ƙasar Andalus da ƙasar Portugal su karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2030 wato nan da shekaru 10 kenan masu zuwa duba da yanzu ana cikin shekarar 2020. Sai dai anasa ran ƙasashen guda biyu zasuyi haɗin gwiwa ne wajen karɓar baƙuncin wannan gasa ta cin kofin duniya.
Hakan ta faru ne bayan shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Andalus wato Luis Rubiales da kuma shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Portugal wato Fernando Gomes sun zauna sun tattauna kuma suka cimma matsaya akan zasuyi wannan haɗin gwiwa domin karɓar baƙuncin gasar nan da shekaru 10 masu zuwa.
Ita dai wannan gasa jujjuyawa takeyi daga nahiya zuwa nahiya inda a dukkanin shekaru 4 akwai nahiyar dazata karɓi baƙuncin gasar, idan ba’a manta ba gasar da akayi wadda ta gabata ta shekarar 2018 ƙasar data karɓi baƙuncin gasar daga nahiyar turai take wato ƙasar Russia inda kuma ƙasar Faransa ta zamo zakara bayan ta lallasa Croatia daci 4 da 2 awasan ƙarshe da suka fafata kuma Faransa ta lashe gasar karo na biyu a tarihi.
Haka zalika a shekarar 2010 ma a nahiyar Afrika aka gudanar da gasar inda ƙasar Afrika ta Kudu ce ta karɓi baƙuncin gasar yayin da ƙasar Andalus ta zamo zakara karon farko a tarihi bayan ta doke Netherland daci 1 da nema, sannan kuma a shekarar 2014 ma a yankin Kudancin Amurka aka gudanar da gasar wato ƙasar Brazil inda Jamus ta zamo zakara bayan ta doke Argentina daci 1 mai ban haushi a wasan ƙarshe.
Wannan gasa maizuwa daza a gudanar ta shekarar 2022 anasa ran ƙasar Qatar ce zata karɓi baƙuncin gasar kuma tuni wannan ƙasa ta Qatar ta shirya tsaf domin ganin anyi wannan gasa a can yankin na Asia kenan, idan ba a manta ba rabonda yankin Asia ya karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya tun a shekarar 2002 wato gasar da aka gudanar a ƙasashen Korea da Japan wanda ƙasar Brazil ta zamo zakara.
Ita dai wannan gasa ta cin kofin duniya an fara bugata tun a shekarar 1930 inda ƙasar Uruguay ce ta fara karɓar baƙuncin gasar kuma itace ta fara zamowa zakara a tarihin gasar, amma kuma yanzu ƙasar Brazil tafi kowacce ƙasa lashe gasar bayan data lashe guda 5.
Anasa ran idan ƙasashen Andalus da Portugal suka karɓi baƙuncin wannan gasa a shekarar 2030 to lokacin gasar cin kofin duniya zata cika shekaru 100 da farawa a duniya bayan da a dai-dai wannan lokaci da ake a shekarar 2020 gasar take bikin cika shekaru 90.