Kulob ɗin Al-Nassr na ƙasar Saudiyya ya yiwa Cristiano Ronaldo, wata gagarumar kyauta.
Kulob ɗin yaba ɗan wasan na ƙasar Portugal agogon da ya kai £630,000 domin murnar zuwan sa kulob ɗin. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bayan kwashe shekara 2 yana tari, matashi ya girgiza da ganin maƙudan kuɗaɗen dake cikin asusun
Cristiano Ronaldo ya koma kulob ɗin ne a cikin watan Janairu, inda ya rattaɓa hannu kan kwantiragin £175m duk shekara.
Ronaldo, mai shekara 37 a duniya an yi masa kyautar agogo mai ɗan karen tsada ƙirar ‘Jacob and Co’, domim yin murnar zuwan sa Al-Nassr.
Agogon wanda aka yi da launin kore domin nuna tutar Saudiyya da addinin Musulunci, an sanya duwatsu masu daraja guda 338 a cikin sa, da farin zinare.
Ronaldo ya nuna wannan dan ƙareren agogon wanda aka yi masa kyautar sa a shafin sa na Instagram.
Ronaldo yana da agoguna masu tsada da kuɗin su ya kai £5m waɗanda suka haɗa da Franck Muller (£1.6m) da Rolex GMT-Master II (£400,000).
Martanin Al-Nassr Bayan Cristiano Ronaldo Ya Gaza Ci Mata Kwallo
A wani labarin na daban kuma, mai horar da ƴan wasan Al-Nassr yayi martani bayan Ronaldo ya gaza zura kwallo a wasan sa na farko a kulob ɗin.
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr, Rudi Garcia, ya yi ikirarin cewa dan wasan gaba Cristiano Ronaldo ya inganta kungiyar duk da cewa ya kasa zura kwallo a raga a wasan da kungiyar ta buga da Ettifaq ranar Lahadi.
Garcia ya ce kasancewar Ronaldo ba ya ba da tabbacin samun nasara ta atomatik a Saudi Pro League bayan Al-Nassr ta doke Ettifaq, godiya ga burin da Anderson Talisca ya ci.